Dakarun Siriya na yunkurin kwance damarar 'yan tawaye
March 19, 2012Manyan tankokin yakin dakarun Siriya da dama ne suka kutsa zuwa birinin Dair al-zour inda mafi yawan al'ummarsa 'yan sunni ne, a wani sabon yunkuri na neman anshe mahimman yankunan da ke karkashin jagorancin dakarun 'yan tawayen masu zaman kansu wadanda ke cigaba da kara himma wajen kai hari kan dakarun gwamnati, kamar yadda shaidu suka bayyana.
Tankoki da motocin yakin masu sulke sun shiga birnin daga arewaci inda 'yan tawayen suka rika nuna turjiyayi a yayin da suke janyewa zuwa ungwanin da ke kudu maso gabashin birnin wadanda ke zaman inda dakarun nasu suka fi karfi.
A yayinda hakan ke faruwa a waje guda kuma wata tawaga ta musamman da manzon hadin gwuiwa na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Hadin Kan Larabawa a rikicin Siriyar, Kofi Anan ya aika kasar ta isa, kuma zata kasasnce a Siriyar har sai sadda aka fara samun ci-gaba wajen ayyukan da zasu kawo karshen zud da jinin da ke gudana ba kakkautawa.
Ahmad Fawzi wanda yayi magana a madadin Kofi Anan, ya fadawa kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP cewa ba zai iya fayyace cikakken shirin da tawagar zata aiwatar a Siriyar ba kuma ziyarar da Anan zai sake kaiwa ya dogara ne a kan cigaban da aka samu daga ayyukan 'yan Siriyar da na tawagar da ta isa yanzu.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Abdullahi Tanko Bala