Dakarun Siriya na gab da kwace Palmyra | Labarai | DW | 26.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Siriya na gab da kwace Palmyra

Sojojin gwamnati da rakiyar jiragen saman yaki na Siriya na gab da kwace garin Palmyra daga hannun mayakan kungiyar IS.

Sojojin gwamnatin Siriya da ke samun tallafin jiragen saman yaki sun kutsa garin Palmyra, abin da ke zama yunkuri mafi girma na sake kwato garin daga tsagerun kungiyar IS masu ikirarin neman kafa daular Islama.

Wata kungiyar kare hakkin dan Adam mai saka ido kan rikici na Siriya, ta ce tuni sojojin gwamnati da tallafin mayakan sa-kai suka kwace galibin yankunan da ke kewaye da garin na Palmyra. Haka wata tashar talabijin mai goyon bayan gwamnatin Siriya ta nuna tankokion yaki na sojoji suna ba ta kashi a kan hanyar shiga garin.

Kwace garin na Palmyra daga mayakan IS zai zama wata gagarumar nasara ga gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad na kasar ta Siriya, wadda take samun tallafin kasar Rasha, bisa yakin basasa da ke faruwa a cikin kasar.