Dakarun SDF sun kaddamar da farmaki a Raqqa | Labarai | DW | 06.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun SDF sun kaddamar da farmaki a Raqqa

Dakarun na Larabawa da na Kurdawa da ke samun goyon bayan Amirka sun kaddamar da wani babban farmaki domin sake kwato garin raqqa na siriya cibiyar Kungiyar mayakan IS.

Dakarun na kawance na SDF wadanda suka ja dagga  a garin Ain Isa da ke da nisan  kilomita 50 daga arewacin birnin na Raqqa sun yi shelar samun nasara nan ba da dewa ba.Yau kusan shekaru biyu da rabi ke'nan da birnin na Raqqa na Siriya ke cikin hannun dakarun na Kungiyar IS.Kuma wannan farmaki na zuwa ne a daidai lokcin da ake kokarin korar 'yan ta'addar na IS daga daya tungarsu da ke a birnin Mosul na Iraki.