1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Najeriya sun ceto mutum 149

April 8, 2018

Dakarun Najeriya, sun sanar da ceto wasu mata da kananan yara masu yawa wadanda mayakan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da su a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/2vgx0
Niger Flüchtlinge aus Nigeria
Hoto: DW/A. Cascais

Dakarun gwamnatin Najeriya, sun tabbatar da kubutar da wasu mata da kananan yara 149 wadanda mayakan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da su a kauyen Yerimari Kura, na jihar Borno. Sanarwar da sojin kasar suka yada a wannan Lahadi, ta ce sun ceto mutanen ne a wani farmaki da suka kai wa mayakan na Boko Haram, inda suka kashe uku tare da kama wasu biyar daga cikinsu a jiya Asabar.

Dakarun na Najeriya sun kuma ce suna bincika lafiyar matan da kuma yaran 149, kamar yadda kakakin mayakan sintirin Lafiya Dole Onyema Nwachukwu ya tabbatar. A share guda kuwa, sun kama wasu 'yan kunar bakin wake biyu a kauyen Mandanari a jiyan, sai dai daya daga cikinsu ya mutu lokacin da jigidar bama-baman da ke a jikinsa ta tashi, akwai wasu fararen hula uku da suka ji rauni.