1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Mongolia zasu kare kotun Majalisar Dinkin Duniya a Saliyo

January 8, 2006
https://p.dw.com/p/BvDB

Wata tawagar dakarun kasar Mongolia mai sojoji 250 ta karbi ragamar ba da kariya ga jami´an kotun MDD mai shari´ar masu aikata laifukan yaki a kasar Saliyo. A cikin wata sanarwa da ta bayar, MDD ta ce tawagar ta Mongolia zata kasance karkashin kwamandan rundunar kiyaye zaman lafiyar majalisar da ke Liberia, makwabciyar Saliyo. Ita ma dai Liberia na kokarin farfadowa daga wani mummunan yakin basasan da ta yi fama da shi wanda ya kawo karshe a cikin shekara ta 2003. Dakarun Mongolia dai su kadai zasu kansance sojojin MDD da suka saura a Saliyo bayan da gamaiyar ta kasa da kasa ta kawo karshen aikin wanzar da zaman lafiya lokacin da ta janye dukkan dakarunta daga kasar dake yammacin Afirka a ranakun karshe na shekara ta 2005.