Dakarun Libiya sun samu nasara kan IS | Labarai | DW | 18.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Libiya sun samu nasara kan IS

Sojoji da ke biyayya ga gwamnatin Libiya da kasashen duniya ke mara wa baya, sun samu galaba a kan mayakan IS a kusa da birnin Misrata.

Dakaru masu biyayya ga gwamnatin Libiya wadda ke samun tallafin kasashen duniya sun samu nasara kan mayakan kungiyar IS da ke ikirarin neman kafa daular Islama a garuruwa uku na yammacin birnin Misrata, abin da ya janyo tarnaki ga nasarori da tsagerun kungiyar IS suka samu a baya.

Yanzu haka dakaraun gwamnatin na fafatawa da tsagerun na IS a wani waje da ke da nisan kilo-mita 50 daga birnin Sirte da ke zama tungar kungiyar. A wannan Laraba kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta zargi 'yan kungiyar ta IS da aikata laifukan yaki inda take kashe fararen hula a birnin na Sirte.

Kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka ta tsunduma cikin rikicin tun shekara ta 2011, bayan juyin-juya halin da ya kawo karshen gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40. Lamura sun kara dagulewa lokacin da aka samu gwamnatoci biyu masu adawa da juna a tsakiyar shekara ta 2014.