1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Lebanon sun kaddamar da hari kan sansanin yan gudun hijira

Sojojin Lebanon suna ci gaba da lugudan wuta a kudancin Lebanon a kokarinsu na kawo karshen tarzoma a sansanin yan gudun hijira na Nahr al bared.Sojoji 4 sun rasa rayukansu guda kuma ya samu rauni.

Rahotanni sunce tun farko ya kungiyar Fatah al Islam sun kashe sojoji 2 wanda hakan ya ingiza sojojin kai masu wannan hari.

Wadanda suka ganewa idanunsu sunce dakarun na Lebanon suna kai hare haren ne ta dukkan bangarori na sansanin.

Akalla mutane 209 suka rasa rayukansu tun fara rikicin makonni 8 da suka shige,fada mafi muni tun yakin basasan kasar a 1975.