Dakarun kawance sun sake halaka mayakan Taliban a Afghanistan | Labarai | DW | 30.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun kawance sun sake halaka mayakan Taliban a Afghanistan

A farmakin da suke kaiwa mayakan Taliban, dakarun dake karkashin jagorancin Amirka a Afghanistan sun sake halaka ´yan tawaye 14 da ake zargin cewa masu kishin Islama ne. Rundunar sojin Amirka ta sanar da cewa an gano ´yan tawayen ne dauke da manyan makamai a lardin Nuristan dake gabashin Afghanistan. A wata musayar wuta da aka yi a lardin Kandahar dake kudancin kasar kuma an kashe wani dan tawaye daya. A makonnin da suka wuce dakarun da Amirka kewa jagoranci suka fara kai farmaki akan sansanonin ´yan tawaye Taliban dake kudanci da kuma gabashin Afghanistan.