1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Izraela sun kutsa gaza

Zainab A MohammedJune 28, 2006
https://p.dw.com/p/Btza
sojojin Izraela a Gaza
sojojin Izraela a GazaHoto: AP

Tankunan izraela ta jiragen yaki kirar saukar ungulu sun kutsa zirin Gaza da safiyar yau,wanda ke bayyana dadin matsin lamba wa sojojin sakai na palasdinu,su saki sojin Izraelan suka cafke ranar lahadi.

A wani abunda ke zama tsauraran gargadi adangane da bukatar sakin jamiin sojin na izraela mai shekaru 19 da haihuwa,prime minister Ehud Olmert,ya bayyana cewa dakarun zasu cigaba da kutsawa cikin yankunan palasdinawan cikin kwanaki masu gabatowa.

Mazauna garin Rafah dake kudancin Gazan dai najin gurnanin bindigogin machine gun,wanda yazo kasa da shekara guda da janyewan dakarun izraelan daga wannan yanki,bayan mamaye na shekaru 38.

Kawo yanzu dai babu arangama.Sai dai dakarun na Izraela dake kewaye da filin saukan jiragen sama na Gaza da aka daina amfani dashi na cikin shirin kota kwana,a dangane da yiwuwar sakin kofur Gilad Shalit,da sojin sakan Palasdinun ke tsare dashi,ba tare da musayar wuta ba.Ajawabinda yayi ta kafofin yada labaru a birnin Kudus,Premier Ehud Olmert ya bayyana cewa,sojojin Izraelan basu da muradin tayar da fada ko kuma sake mamayen zirin Gaza,makasudun zuwansu wannan yanki shine ganin cewa an sako Gilad,tare dayi masa rakiya gida cikin koshin lafiya.

A harin farko da suka kaddamar kwanaki uku bayan barkewan wannan rikici,jiragen yakin izraila sun tarwatsa gadoji guda uku ,a wani abunda suka bayyana dacewa,hanyar dakatar da sojojin sakan daka tafiya da kamammen sojin na Izraela.

Bugu da kari Jirgin yakin Izraela ya kaiwa cibiyar samarda wutan lantarki guda daya dake Gaza hari,inda nan take wuta ta tashi,wanda kuma ya dakatar da wutan lantarki a wannan yanki dake da mazauna million 1 da dubu dari 4.Inginiyoyi sun sanar da cewa gyaran cibiyar wutan lantarkin zai dauki watanni shida.

Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya bayyana wannan hari akan fararen hula da kasancewa,take hakkin jamaa da hukuntasu kan laifin da basu da masaniya.

Shi kuwa danmajalisar gwamnatin Hamas Mushir al-Masri,yace wannan mataki da Premier Olmert ya dauka ,bazai haifar da komai ba,domin zai dada dasa ayar tambaya adangane rayuwar sojin Izraelan dake hannun sojin sakan na Palasdinu.

A hannu guda kuma larabawa dake yankin gabas ta tsakiya sunyi Allah wadan wadannan hare hare da dakarun izraelan suka kaddamar a zirin gaza,duk dacewa shugabannin kasashen larabawan a asirce,na kokarin ganin cewa an saki sojin na Izraela.A birnin Alkhahiran masar,gwamnati na kokarin tattauna yiwuwar sakin palasdinawa dake hannun Izraelan a matsayin musayan,sakin sojinsu dake hannun palasdinawa.

Ita kuwa kungiyar gamayyar turai EU,kira tayi ga bangarorin biyu dasu tsagaita wuta ,domin bawa matakin diplomasiyya hanyar warware wannan rikici.Kwamissinan harkokin waje na kungiyar,Benita Ferrero-Waldner tace kawanyan da dakarun izraelan sukayi wa zirin gaza da harin da suka kai cibiyar wutan lantarki ,zai jefa asibitoci da halin rayuwan alummar palasdinun cikin hali mawuyaci.