1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Isra’ila sun kashe wani kwamandan ƙungiyar Hamas a zirin Gaza.

November 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bub0

A wani ɗaukin da suka gudanar cikin daren jiya, dakarun Isra’ila sun bindige wani kwamandan ƙungiyar Hamas har lahira a zirin Gaza. Wata sanarwar da ƙungiyar ta bayar ta ce a cikin daren ne wani rukunin Isra’ilan ya mamaye gidan kwamandan, Wael Hassanin, inda aka yi ta musayar wuta tsakanin mayaƙan Hamas ɗin da dakarun Isra’ilan. A wannan fafatawar ne suka harbe kwamandan.

Har ila yau dai a zirin Gazan, wani harin rokoki da jiragen saman yaƙin Isra’ilan suka kai kan wata mota a gabashin birnin Gazan ya janyo asarar rayukan Falasɗinawa biyu da kuma jin raunin fararen hula 6, a cikinsu har da yara ƙanana guda biyu. Ƙungiyar Hamas ta ce mutanen da suka rasa rayukansun mayaƙansu ne daga rukunin baraden al-Qassam. Ita dai Isra’ilan ta ce ta harba rokoki kan motar ne saboda tana ɗauke da ’yan ta’adda.