Dakarun Isra’ila sun kashe wani ɗan ta kifen Falasɗinawa a Gaɓar Yamma. | Labarai | DW | 16.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Isra’ila sun kashe wani ɗan ta kifen Falasɗinawa a Gaɓar Yamma.

Dakarun Isra’ila sun bindige wani ɗan ta kifen Falasɗinawa har lahira, a wani sansanin ’yan gudun hijira da ke kusa da garin Nablus a arewacin Gaɓar Yamma. Jami’an tsaron Falasɗinawa sun ce ɗan ta kifen, mai shekaru 25 da haihuwa, ɗan ƙungiyar jama’a ta ’yanto Falasɗinu ne, wato PFLP a taƙaice.

A halin da ake ciki dai, jiragen sama masu saukar ungulun Isra’ilan sun kai hare-haren rokoki kan wasu gidaje biyu da suka ce na ’yan ta kifen Falasɗianawa ne a Zirin Gaza. Waɗannan hare-haren kuwa, sun zo ne sa’o’i kaɗan bayan da mayaƙan Falasɗinawan suka yi wa garin Sedrot da ke cikin Isra’ilan hadarin rokoki, inda suka kashe wata mace ’yar ƙasar Bani Yahudun, sa’annan kuma suka ji wa wasu mutane biyar rauni.