Dakarun Israila sun kashe masu sa ido na majalisar dinkin duniya | Labarai | DW | 26.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Israila sun kashe masu sa ido na majalisar dinkin duniya

Jiragen yakin Israila sun kai hari kan cibiyar agaji ta majalisar dinkin duniya inda jamianta 4 suka rasa rayukansu a yayinda ake bude babban taro a Rome akan rikicin yankin gabas ta tsakiya.

Sakatare janar na majalisar Kofi Annan ya bukaci Israila data gudanar da bincike game da wannan hari da ya baiyana cewa dama da niyar kaiwa kann cibiyar agaji ta majalisar a kudancin Lebanon.

Israilan ta sanarda cewa zatayi bincike kann harin sai dai ta baiyana mamakinta cewa Kofi Annan zaiyi tunanin cewa da gangan aka kai harin kann jamin majalisar.