Dakarun Isra’ila sun kai wani sabon hari a Zirin Gaza. | Labarai | DW | 12.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Isra’ila sun kai wani sabon hari a Zirin Gaza.

Rahotannin da muka samu daga yankin Gabas Ta Tsakiya sun ce sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa 4, a cikinsu har da wani ɗan yaro matashi, a wani harin fda suka kai cikin daren jiya a Zirin Gaza. Falasɗinawan dai sun rasa rayukansu ne yayin da dakarun ƙasar Bani Yahudun, da kuma jiragen sama masu saukar ungulunsu, suka afka wa ƙauyen Abassan a daren na jiya. Kawo yanzu dai, ba a ba da wasu bayanai kan sauran mutane ukun da dakarun suka halaka ba. Wannan harin, shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren da Isra’ilan ta fara kaiwa a Zirin Gazan tun watanni 4 da suka wuce, bayan cafke wani sojin Isra’ilan da Falasɗinawan suka yi. Tun wannan lokacin kawo yanzu dai, kusan Falasɗinawa 230 ne suka rasa rayukansu, mafi yawanus kuma, fararen hula ne.