Dakarun Isra’ila sun harbe wasu shugabannin `yan ta kifen Falasdinawa guda biyu har lahira a Zirin Gaza. | Labarai | DW | 02.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Isra’ila sun harbe wasu shugabannin `yan ta kifen Falasdinawa guda biyu har lahira a Zirin Gaza.

Jiragen saman yakin Isra’ila sun kai hare-hare a zirin Gaza, inda suka halakad da da wasu shugabannin `yan ta kifen Falasdinawa guda biyu a cikin motarsu. A kalla, fararen hula guda 10 ne kuma rahotanni suka ce sun ji rauni, yayin da motar ta yi bindiga kusa da sansanin `yan gudun hijiran Jabaliya da ke arewacin Zirin Gazan.

A cikin wata sanarwar da ta bayar, kungiyar islaman nan ta Hamas ta ce Isra’ila ta fara wani sabon yaki kuma, inda take farautar Falasdinawa dai-dai tana halaka su. Wata kungiyar kuma, wato ta baraden al-Aqsa, ta ce za ta janye daga tsagaita wutar da aka yarje a kansa. A halin da ake ciki kuma, an yi wata kazamar fafatawa tsakanin dakarun Isra’ila da kungiyoyin Falasdinawa a garin Jenin da ke Gabar Yamma, yayin da sojojin kasar bani Yahudun suka mamaye wani ginin da `yan bindigan kungiyar islamic Jihad ke ciki. Tun makon da ya gabata dai, Isra’ila ta yi ta kai hare-hare a kan kungiyoyin Falasdinawa, sakamakon wani harin kunan bakin waken da kungiyar islamic Jihad din ta ce ita ta kai a cikin Isra’ilan.

A wata sabuwa kuma, wani rahoton da muka samu dazu-dazun nan, ya ce `yan bindigan Falasdinawa sun harbe wani sojan Isra’ila da ke sintiri yau da safen nan a arewacin Gabar Yamma.