1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Isra’ila sun cafke wani babban ɗan majalisar Falasɗinawa.

Dakarun Isra’ila, sun cafke sakataren Majalisar Falasɗinu, Mahmud al-Ramhi a gidansa da ke garin El-Bireh, kusa da birnin Ramallah a Gaɓar Yamma. Wani kakakin rundunar sojin Isra’ilan ya tabbatad da rahotannin da suka nuna hakan. Shi dai Ramhi, shi ne wani babban jami’in Hukumar Falasɗinu na baya-bayan nan da Isra’ilan ta cafke, a jerin manyan jami’an Falasɗinawan da ta yi ta kakkamawa tun harin da ’yan ta kifen Falasɗinawan suka kai kan iyakar zirin Gaza da Isra’ilan a ran 25 ga watan Yuni, inda suka kashe sojojin ƙasar Bani Yahudun guda biyu, sa’annan kuma suka yi garkuwa da ɗaya. A jiya ma sai da dakarun Isra’ilan suka kame mataimakin Firamiyan Falasɗinawan, Nassereddin al-Shaer, wanda kuma yake ɗaya daga cikin ƙusoshin ƙungiyar Hamas.