1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Isra’ila sun bindige wasu ’yan bindigan Falasɗinawa guda biyu, a wata fafatawar da suka yi a garin Nablus.

May 17, 2006
https://p.dw.com/p/Buxz

Falasɗinawa biyu ne rahotanni suka ce sun rasa rayukansu, a wata fafatawar da ’yan bindigan ƙungiyar nan ta Islamic Jihad suka yi da sanyin safiyar yau da dakkarun Isra’ila, a garin Nablus da ke Gaɓar Yamma. Ɓangarorin biyu, sun fara buɗe wa juna wuta ne, yayin da dakarun Isra’ilan suka kewaye wani gini a garin na Nablus, don neman su kame wani ɗan ƙungiyar Islamic Jihad ɗin, wanda suke nema kamar ruwa a jallo.

Jami’an kiwon lafiyar Hukumar Falasɗinawa da suka shiga cikin ginin, sun ce sun sami ɗaya daga cikin ’yan ƙungiyar kwance da mummunan rauni, sa’annan sun kuma gano gawawwakin takwarorinsa guda buiyu. Wani likitan Falasɗinawa, Dr. Ghassan Hamdan, wanda ya kasance a gun, ya faɗa wa maneman labarai cewa, sojojin Isra’ilan sun yi awon gaba da gawawwakin da kuma mutumin da ya ji raunin.

Rahotannin dai sun ce an ci gaba da fatatawa a duk tsawon safiyar ta yau a yankin, kuma dakarun Isra’ilan sun rusa wani bangaren ginin da ’yan bindigan ke ciki. Bini bini, sojojin ƙasar bani Yahudun na kai hare-hare a yankunan Gaɓar Yamman don cafke ’yan ta kifen Falasɗinawa.