Dakarun Isra′ila na ci gaba da kai hari a Zirin Gaza | Labarai | DW | 03.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Isra'ila na ci gaba da kai hari a Zirin Gaza

Dakarun Isra’ila a arewacin Zirin Gaza sun kashe wasu Palasɗinawa bakwai a daren jiya cikinsu kuwa har da wasu ‘yan kungiyar Hamas su uku. Majiyoyi daga cibiyoyin kula da lafiya na Palasɗinawa sun ce harin da dakarun Isra’ila suka kai da helikopta a birnin Gaza ya halaka wasu sojojin sa kai su shida da fararen hula 11. Wata mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun kai harin ne a Gaza bayan buɗe musu wuta da aka yi tun farko a wannan yanki. Kusan a kowace rana dakarun Isra’ila suna ci gaba da kai hari a Zirin Gaza tun lokacin da ƙungiyar Hamas ta kame yankin a watan Yuni na 2007 bayan ta fatattaki dakarun dake goyon bayan ƙungiyar Fatah ta shugaba Mahmud Abbas.