1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Isra’ila na ci gaba da ɗaukinsu a zirin Gaza.

A rana ta huɗu a jere ta ɗaukin da dakarun Isra’ila ke yi a zirin Gaza, rahotanni sun ce sun kashe Falasɗinawa 10 cikin daren jiya, a wata kutsawar da suka yi a garin Beit Hanoun da ke arewacin zirin. Isra’ilan dai ta ce tana fatattakar masu harba mata rokoki ne daga wannan yankin. Wata sanarwar da hukumar sojin ƙasar ta bayar ta ce dakarun sun kashe wani babban mai ƙera rokoki na Falasɗinawan. Kawo yanzu dai, yawan Falasɗiwana da suka rasa rayukansu sakamakon ɗaukin baya-bayan nan da dakarun Isra’ilan ke yi a zirin Gaza ya tashi zuwa 44.