Dakarun Habasha sun sake kutsawa cikin Somaliya. | Labarai | DW | 20.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Habasha sun sake kutsawa cikin Somaliya.

Wasu rahotannin da ke iso mana daga ƙasar Somaliya sun ce mazauna kewayen garin Baidoa sun tabbatar da ganin ayarin motocin dakarun Habasha guda 11 ɗauke da sojoji kusan ɗari 3 a garin Awdiinle, mai nisan kimanin kilomita 30 daga Baidoa, inda gwamnatin wucin gadin Somaliyan ke da mazauninta.

Tun cikin watan Yulin da ya gabata ne dai, ake zaton Habashan ta tura dubban dakarunta zuwa Somaliyan, don kare gwamnatin riƙon ƙwarya ta shugaba Yusuf Abdullahi daga hannun mayaƙan ƙungiyoyin islama da tuni suka kame birnin Mogadishu, suke kuma ƙoƙarin maido da yankunan kudancin ƙasar ƙarkashin ikonsu. Mahukuntan Habashan dai sun sha ƙaryata rahotannin da ke nuna cewa sun tura dakaru a Somaliyan.