Dakarun Habasha sun fara janyewa daga Mogadishu | Labarai | DW | 23.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Habasha sun fara janyewa daga Mogadishu

Dakarun kasar Habasha sun fara janyewa daga birnin Mogadishu,makonni hudu bayan sun taimakawa gwamnatin wucin gadin kasar korar mayakan islama daga babban birnin kasar wato mogadishu..

Ministan harkokin cikin gida na Somalia Hussein Muhammad Farah Aideed yace dakarun kungiyar taraiya Afrika AU zasu maye gurbin sojojin na Habasha cikin mako guda mai zuwa.

Kungiyar ta AU ta amince da aikewa da dakarunta kusan 8,000 zuwa kasar ta Somalia,kodayake babu tabbacin cewa ko zasu iya tabbatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar da take fama da rikici tun 1991.