1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

dakarun gwamnatin Sri Lanka sun kai hari kan ´yan tawayen Tamil Tigers

Kwana hudu a jere jiragen saman yakin gwamnatin Sri Lanka sun yi lugudan wuta akan sansanonin ´yan tawayen Tamil Tigers dake gabashin kasar. Wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta bayar ta ce yanzu sun sake bude hanyoyin kaiwa ga wurare samar da ruwa a yankin. To amma wani kakakin ´yan tawayen ya ce har yanzu ana gwabza fada don kame yankin. Kimanin ´yan tawaye 7 ne aka kashe a wannan gumurzu. Yanzu haka dai fadan da ake yi tsakanin gwamnatin Sri Lanka da ´yan tawaye ya kara tabarbarewa. Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu suka kulla, a bana kadai an halaka mutane kimanin 800 sakamakon hare hare da kuma batakashi da suke yi.