Dakarun Chadi sun halaka ´yan tawaye 300 a kan iyakarta da Sudan | Labarai | DW | 20.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Chadi sun halaka ´yan tawaye 300 a kan iyakarta da Sudan

Jami´an kasar Chadi sun ce dakarun gwamnati sun kashe mutane sama da 300 a matakan da suka dauka na murkushe wani harin ´yan tawaye a garin Adre dake kan iyakar Chadi da Sudan. A cikin wata sanarwa da ya bayar, ministan harkokin wajen Chadi Ahmat Allam-Mi ya ce an fatattaki sauran ´yan tawayen har zuwa wani yankin kan tsaunuka dake cikin Sudan. To sai dai majiyoyin gwamnati sun ce har yanzu ana ci-gaba da daukar matakan soji a yankin da ke ciki da wajen garin Adre mai nisan kilomita kimanin dubu daya gabas da N´djamena babban birnin kasar.