1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Burkina Faso sun kashe 'yan ta'adda

Binta Aliyu Zurmi
September 3, 2023

Rahotanni daga Ouagadougou na kasar Burkina Faso na nuni da cewar sojoji sun sanar da hallaka sama da mayakan jihadi 100 a wasu tagwayen harin sumame da ka kai a maboyarsu da ke kan iyakokin Mali da Nijar.

https://p.dw.com/p/4VttA
Burkina Faso | PK Ibrahim Traore
Hoto: AA/picture alliance

A sanarwar da sojojin suka fitar da yammacin jiya sun ce, lamarin ya auku ne a ranar Juma'ar da ta gabata, kuma sun yi nasarar lalata motoci da mashinan 'yan ta'addar gami da kwace manyan makamai da magunguna, su kuma a nasu bangaren sun yi asarar jami'ansu 5.

Kasar Burkina Faso da ke yammacin Afirka ta jima tana fama da ayyukan wadannan mayakan da ke da alaka da kungiyoyin al-Qaeda da IS.

A baya shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traoré ya tabbatar da karfin 'yan ta'adda da ke haddasa tashin hankali a kasar ya karu matuka.

Sama da mutum miliyan biyu ne rikicin 'yan ta'addar kasar Burkina Faso ya raba da matsugunansu yayin da dama suka rasa rayukansu.