1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Amurka sun kutsa kai izuwa Somalia

Jaridar Washinton Post ta Amurka ta rawaito cewa, wasu dakarun sojin Amurka sun kutsa kai izuwa cikin kasar somalia.

Hakan kuwa a cewar jaridar, ya biyo bayan hare hare ne da sojojin suka kaine, izuwa kasar har na tsawon kusan mako daya.

A cewar jaridar, dakarun sojin sun shiga kasar ta somalia ne don tantance yawan mutanen da suka rasa rayukan su, sakamakon irin hare haren da suka kai izuwa kudancin kasar.

A cewar rahotanni dai wadannan hare hare dai ana kai su ne da sunan halaka jami``an kungiyyar Alqaida , da aka ce na da mafaka a kasar ta somalia ne.