Dakarun Amurka sun kai hari kan farar hula a Iraqi | Labarai | DW | 05.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Amurka sun kai hari kan farar hula a Iraqi

Dakarun sojin kasar Amurka sun kashe akalla mutane 17 cikinsu da mata da yara yau jumaa cikin wani hari a arewa maso gabacin Bagadaza.A cewar jamian sojin jirgin saman yakin Amurka ya kai hari kann kungiyar wasu mutane da suka zaci sojojin sa kai ne,bayan sun hango mutum guda dauke da makami a hannunsa.Sun kai wannan hari ne a cewarsu kann wani komandan yan shia da ake zargi da yin sumogan makami daga Iran zuwa Iraq.Wannan hari dai ya faru ne kuma adai dai lokacinda ake takunsaka tsakanin Iran da Amurka bayan tsare Mahmudi Farhadi dan kasar Iran makonni biyu da suka shige.Komandojin Amurka suna zarginsa da kasancewa memba na rundunar sojin juyin juya hali na Iran kuma yana taimakawa sojin sa kai yan shia a kasar Iraq.