1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Amurka a Iraki

Umaru AliyuFebruary 26, 2008

Sharhi kan kamfanin Blackwater a Iraki

https://p.dw.com/p/DDoO
Tambarin kamfanin tsaro na Blackwater.Hoto: picture-alliance/ dpa

Farar hula yan Iraki goma sha bakwai ne aka kashe a watan Satumkba na bara, wasu ashirin da hudu kuma aka ji masu rauni, lokacin da Amerikawa dauke da makamai suka kutsa dandalin Nissur a Bagadaza, suka bude wuta kan wadanda sukai zaton yan bindiga dadi ne. Ko da shike wannan hadari ba shine irin sa na farko ba, amma aukuwar sa ya haddasa zaman musamman a majalisar dokokin Amerika,domin sauraron bayani game da aiyukan kamfanin Blackwater a Iraki. Majalisar a karon farko ta maida hankalin ta ga aiyukan kamfanin dake daukar hankali a kafofin yada labarai na Amerika da na duniya baki daya, wanda har ya zuwa wannan lokaci babu wanda ya damu dashi, musammanm a Irak da Afghanistan da sauran yankunan da ake fama da rikici cikin su, inda Amerika ta shigar da wadanda ta kira, jami'an tsaro.
Mawallafin nan na Amerika mai suna Jeremy Scahill yayi amfani da aiyukan wannan kamfani da aka fi takaddama a game da aiyukan sa, domin rubuta wani littafi da ya sanya masa suna Blackwater, bunkasar kamfani mafi girma da karfi dauke da sojoji masu zaman kansu a duniya.
A bayan sojoji dubu dari da hamsin da Amerika take dasu a Iraki,, gwamnatin Bush ta kuma tura wasu sojojin masu zaman kansu kimanin dubu dari zuwa can, wadanda dubbai daga cikin su akai masu cikakken shiri na damarar makamai, a matsayin sojojin haya a kasar ta Irak. Daya daga cikin kamfanonin tzsaro da suka fi karfi dake aiyukan su a Irak, shine kamfanin Blackwater.
Sojojin na Blackwater suna samun horon su ne a wani wuri mai fadin murabba'in kilomita arba'in da biyar mai cike da fadamu, abin da ma ya sanya aka sanwa kamfanin suna Blackwater. Sojojin wannan kamfani suna aiyukan sune a Irak, domin kare gine-gine da muhimman mutane, kamar jami'an diplomasiyar Amerika a kasar tare da kare wuraren samar da man fetur ko bututun man fetur daga aiyukan yan sari ka noke. Erik Prince, wanda shine ya kafa kamfanin Blackwater, ya shaidawa majalisar dokokin Amerika bayani a game da yadda rayuwas take a kasar ta Irak.
YaceA kullum rana ta Allah akan kaiwa motoci da sauran ababen hawa harbi, har yadda ba ma zamu iya kidaya irin wadannan hare-hare ba. Da farko idan hakan ya faru, wnada aka kaiwa harin yakan nemi kare kansa. Yawancin hare-haren da mukan shaidar a Irak suna da rikitarwa. Hakan yana nufin a bayan harin bom, wadanbda suka kai harin sukan kuma bude wuta a lokaci guda. Yan bindiga dadi a Irak sun yi imanin cewar suna iya samarwa kansu suna ta hanyar kisan Amerikawa dake kasar.
Kamfanin Blackwater ana kara kwatanta ma'aikatan ta a matsayin sojojin haya, to amma Gerhard Kümmel bai yarda da wnanan bayani ba, domin kuwa a bisa ra'ayin sa, sojojin haya mutane ne dake aiyukan su dai-dai, wadanda saboda neman ribar kudi, sukan mika kansu ga bukatun sojojin wata kasa da ba tasu ba.
To sai dai a game da Irak ko Afghanistan yana da wuya a banbance tsakanin aiyukan tsaro da shiga yakin da ake yi a kasashen biyu kai tsaye. BIsa aiki da tsarin dokokin duniya, ma'aikatan Blackwater ba sojojine dake shiga yaki kai tsaye ba. Idan hart aka kama su a matsayin fursunoni yaki, ba za'a basu kariya karkashin yarjejeniyar Geneva da ta kare sojojin da aka kama a matsayin fursunonin yaki ba. Saboda haka ana bnbukatar warware sabani a game da matsayin irin wnanan runduna ta Blackwater. Wannan kuwa, kamar yadda Gerhard Kümmel ya nunar, abu ne da zai dauki lokaci , duk kuwa da ganin cewar majaisar dinkin duniya ta dauki labarin a hanun ta.
Yace majalisar dinkin duniya a da can ma ta taba daukar irin wannan mataki, inda a shekaru na saba'in ta gabatar da tsarin dokokin da suka shafi aiyukan sojojin haya a duniya baki daya, wadanda suka maida hankalin su ga aiyukan irin wadannan kamfanoni masu sojojin hana na kashin kansu, ko kuma sojoji masu tsaro, kamar Blackwater.
Abin da har yanzu ba'a sani ba shine matsayin Jamus ko shigar Jamusawa a irin wadannan kamfanoni na tsaro kamar Blackwater. Yan kadan ne kawai daga cikin ma'aikatan kamfanin suka fito daga Amerika. Sauran kuma an dauke su ne daga yankunan dniya dabam dabam, ciki kuwa har da Jamus.