Dakarun Amirka a Iraqi, sun fara wani ɗauki a garin Ramadi. | Labarai | DW | 18.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Amirka a Iraqi, sun fara wani ɗauki a garin Ramadi.

Mazauna garin Ramadi, wanda ake zato kamar yana ɗaya daga cikin muhimman ramin kurar ’yan tawayen Iraqi, sun ce dakarun Amirka sun yi wa garin ƙawanya da daddatase duk hanyoyi shiga ko fita daga cikinsa. Wata kakakin rundunar sojin Amirkan a Iraqi, ta tabbatad da cewa wani ɗauki na ci gaba a garin, amma ba ta ba da ƙarin haske game da burin dakarun ba. A farkon wannan watan dai, sai da wani kakakin sojin Amirkan ya bayyana cewa ƙungiyar al-Qaeda ta sake yaɗa angizonta a Ramadin. Sabili da haka, za a tura wani rukunin da ya ƙunshi sojojin ƙundumbala dubu da ɗari 5, don su ƙwato garin daga hannunta.

A wata sabuwa kuma, hukumar rundunar sojin Amirka a Iraqin, ta tabbatad da rahotannin da ke nuna cewa, wani sojan Amirka ya sheƙa lahira a birnin Bagadaza a ran juma’ar da ta wuce, yayin da wata nakiyar da aka dasa a gefen titi, ta yi bindiga kusa da motar da yake ciki. Hakan kuwa, ya kawo yawan sojojin Amirkan da suka rasa rayukansu a Iraqin tun shekara ta 2003, zuwa dubu biyu da ɗari 5 da biyu, a hukumance.