1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Amirka a Iraqi, sun ce sun kashe ’yan tawaye 16 a wani ɗauki da suka yi a kewayen birnin Bagadaza.

May 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuyM

Hukumar rundunar sojin Amirka a Iraqi, ta ba da sanarwar cewa wani rukuninta da ya kunshi sojojin igwa da mayaƙan sama cikin jirage masu saukar ungulu, sun yi wani ɗauki a kewayen birnin Bagadaza, don fatattakar ’yan yaƙin gwagwarmaya da suke ta kai musu hare-hare ba kaƙƙautawa. A cikin sanarawar da ta buga yau a birnin Bagadaza, hukumar ta ce dakarun Amirkan sun kashe ’yan tawaye 16, a cikinsu har da wani shugaban ’yan tawayen da ya jagoranci harbo jirgin sama mai saukar ungulun rundunar a watan jiya, inda sojoji biyu suka sheƙa lahira.

A ɗaukin da rukunin ya fara tun ranar asabar da ta wuce a garin Latifiyah, mai nisan kiloita 30 a kudu daga birnin Bagadaza, rahotanni sun ce ’yan tawaye 2 da fararen hular Iraqi guda 4 ne suka ji rauni, a cikinsu har da yara biyu da wata mace kuma mai juna biyu. Hukumar rundunar sojin Amirkan dai ta kuma tabbatad da rahotannin da ke nuna cewa ’yan yakin gwagwarmayar sun sake harbo wani jirgin sama mai saukar ungulunta a ɗauki ba daɗin da suka yi jiya da dakarun Amirkan a wannan yankkin, inda sojoji biyu suka rasa rayukansu.