1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Amirakawa sun sake kashe fararen hula a Iraki

Dakarun da Amirka ke wa jagoranci sun harba makamin atileri akan tashar jirgin kasar birni Ramadi dake lardin Anbar na yammacin Iraqi, inda suka auna wasu maza 4 dake sauke makamai daga taragon jirgi. To amma jimi´an asibiti sun ce dakarun Amirka sun halaka fararen hula 5 sannan sun yi 15 rauni a birnin Ramadi mai nisan kilomita 115 yamma da birnin Bagadaza. Dakarun da suka kai harin sun musanta cewa an kashe fararen hula ko an yi musu rauni sakamakon wannan harin da suka ce ya cimma manufar sa. A wani labarin kuma rundunar sojin Amirka ta amsa cewar ta halaka fararen hula 3 bisa kuskure yayin wani atisayen soji a arewacin birnin Bagadaza. Wata sanarwa da rundunar ta bayar ta ce wani makami da suka harba ya fada kan wata unguwa da mutane ke zaune a ciki. Sojojin Amirka na shan matsin lamba dangane da zargin da aka yi musu na yiwa wasu fararen hular Iraqi su 24 kisan gilla a garin Haditha a cikin watan nuwamban bara.