1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daidatar huldodi tsakanin Zimbabwe da Assusu bada lamani na Dunia

February 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7q

Assusu bada lamani na dunia, ya bayyana cewar kasar Zimbabwe, ta zuba dalla milion 9, daga jimilar kuddaden da a ka tambayo ta.

Wannan zubi, zai sa assusun ya cenza tunani a game da shawara da ya yanke, ta fida kasar Zimbawe daga sahun membobin sa, a sakamakon kasa bassusukan da ya tambayo ta.

Sai duk da haka, akwai sauran ragowar zunzurutun kudi, da su ka tashi dalla milion 119, da ya kamata a ce kasar ta biya, sannan ga karin dalla milion 273, wanda tukuna har yanzu wa´adin fara biyan su bai cika ba.

Ranar 8 ga watan mai kamawa ne komitin gudanarwa na assusun bada lamani zai zaman taro, domin daukar saban mataki na sake maido Zimbabwe a matsayin memba a cikin sa.