Daidaituwa a taron G8 | Siyasa | DW | 07.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Daidaituwa a taron G8

A taron G8 an cimma daidaituwa akan kare makomar yanayin duniya

Shugabannin kasashen G8

Shugabannin kasashen G8

Duk dai wanda yayi hanganen nesa zai yi madalla da nagartaccen ci gaban da aka samu a zauren taron kasashen G8 da suka fi ci gaban masana’antu a duniya. Domin kuwa a karo na farko wadannan kasashe wadanda sune ainifin ummal’aba’isin dimamar yanayi a duniya, sun fito fili sun hakikance da alhakin da ya rataya wuyansu tare da neman danka wa MDD alhakin tsara wani kudurin da za a wajabta aikinsa akan kowa da kowa bisa tsarin yarjeniyoyi na kasa da kasa domin cimma manufar kayyade yawan hayaki mai gubar dake haddasa dimamar yanayin a duk fadin duniya. A hakika dai tun da farkon fari ba wanda ya saka dogon burin cewar za a cimma wata daidaituwar da ta zarce wannan ko kuma wadda ta gaza hakan. Wannan kuma wata babbar nasara ce ga shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a diplomasiyyance. Domin kuwa sai da tayi naci akan wannan batu ta yadda hatta kasashen Amurka da Japan ba zasu iya kakkabe kansu daga lamarin ba. Dangane da kasashe masu matsakaicin ci gaban masana’antu dai ba lalle ba ne ba su yi biyayya ga kudurin taron kolin, saboda kasashe kamar China da Indiya sun halarci zauren taron ne a matsayin ‘yan kallo kuma a sakamakon haka basu da ta cewa. Amma duk da haka tilas ne wadannan kasashe dake samun bunkasar tattalin arziki, wadanda kuma a cikin ‘yan shekaru masu zuwa zasu kasance tsakanin kasashe masu kazamin lahani ga makomar yanayin duniya, su ba da kai bori ya hau a shawarwarin da MDD zata gabar bisa manufa. Ta la’akari da haka ana iya cewar an samu wani labari mai kwantar da hankali daga zauren taron da ake gudanarwa a yankin shakatawa na Heiligendamm dake gabar tekun eastsea a karkashin tsauraran matakai na tsaro. Gabanin taron dai an fuskanci cece-kucen da ya sanya aka shiga fargabar sake billar wani sabon yanayi na yakin cacar baka tsakanin Amurka da Rasha amma bayan ganawa ta keke-da-keke tsakanin sassan biyu sai aka samu sararawar al’amura, lamarin dake nuna mana muhimmancin shawarwari akan manufa.