Daftarin Tsarin Mulkin Turai | Siyasa | DW | 28.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Daftarin Tsarin Mulkin Turai

A gobe juma'a idan Allah Ya kai mu za a yi bikin rattaba hannu kan daftarin tsarin mulkin Turai a birnin Rom

Tun misalin shekara daya da ta wuce ne aka kaddamar da daftarin tsarin mulkin kasashen KTT mai shafi 350 a kasuwa ta yadda duk wani dan kasa ke da ikon bitarsa filla-filla. Domin kuwa manufar da aka fuskanta tun da farkon fari shi ne ba wa kowa-da-kowa ikon karantawa da kuma fahimtar kundin ba sai kawai malaman shari’a ba. Wannan abu ne dake da muhimmanci matuka ainun in ji ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer, wanda ya kara da cewar:

Daftarin tsarin mulkin na mu na kasashen Turai wani ci gaba ne na tarihi a wannan karnin da muke ciki. Daftarin na da nufin wayar da kan jama’a a game da alherin dake tattare da alkiblar da aka sa gaba da kuma muhimmancin hadin kan kasashen Turai wajen samun ikon taka rawar gani a manufofi na cikin gida da ketare.

A babin gabatarwa na daftarin dai an mayar da hankali ne ga ainifin shikashikan manufar hadin kan Turai, wadanda suka hada da adalci da ‚yanci da girmama hakkin dan-Adam da kuma tabbatar da mulkin demokradiyya a karkashin wani kyakkyawan yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma taimakon juna. A wannan babin dai an samu wasu da suka dage akan lalle sai an shigar da addinin kirista a matsayin daya daga cikin wadannan shikashikai. Amma an fuskanci mummunar adawa game da haka, inda a karshe aka amince da yin nuni da al’adu da kuma addinin da nahiyar Turai ta gada tun daga zamanin kakannin-kaka. Daftarin dai ya fara ne da cikakken sharhi a game da kudurorin KTT da kuma ‚yancin da al’umar kasashen kungiyar ke da shi na zabar daya daga cikin kasashenta domin zama na dindindin daidai da yadda ransa ya raya masa, inda yake da ikon kada kuri’a a zabubbuka na kananan hukumomi da na majalisar Turai. A bangaren hakkin dan-Adam kuwa kusan babu wani banbanci tsakanin abin da daftarin ya tanada da kuma kudurin MDD akan hakkain dan-Adam, ko da yake an yi wani dan kari a wasu bangarori da dama. Akasarin babunan daftarin dai ya shafi ita kanta Kungiyar Tarayyar Turan ce, inda aka yi bayani dalla-dalla a game da manufofinta a fannin siyasa da tattalin arziki ta yadda kowa da kowa zai iya fahimta ba tare da neman karin bayani ba. Kuma kamar yadda aka saba dangane da kowace kungiya, ita ma Kungiyar ta Tarayyar Turai ta tanadi sharuddan da suka shafi karbar sabbin wakilai a inuwarta da kuma matakan takunkumi ko ladabtarwar da za a iya dauka akan kowace kasar dake da wakilci a cikinta idan an same ta da laifuka na keta haddin kudurorin kungiya. Sai dai da aka sha famar kai ruwa rana kafin a cimma daidaituwa akan fasalin da daftarin tsarin mulkin ke dauke da shi a yanzun.