1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daftarin kundin tsarin mulkin kungiyar EU

May 27, 2006
https://p.dw.com/p/BuwV

Ministocin harkokin wajen kasashen KTT wadanda a halin suke wani taro a kasar Austria sun tabbatar da cewa babu wata dama ta ceto kundin tsarin mulkin kungiyar EU gabanin zabukan da za´a gudanar a kasashen Faransa da NL a badi. Kuri´un raba gardama da aka gudanar a kasashen biyu sun yi fatali da tsarin mulkin na kungiyar EU. Ministocin dake taro a birnin Vienna sun jaddada cewar daftarin tsarin mulkin wanda ke da nufin karfafa ikon kungiyar ta EU tare da inganta manufofin ta na ketare, bai mutu ba samsam. To amma fata na kara dushewa game da ko kasashe 25 membobin EU zasu rattaba hannu kan tsarin mulkin kafin ya fara aiki.