Daftarin kariya ga Jamián MDD a Iraqi | Labarai | DW | 03.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daftarin kariya ga Jamián MDD a Iraqi

Amurka da Britaniya sun gabatar da wani daftarin ƙudiri ga kwamitin sulhun majlaisar ɗinkin duniya wanda zai inganta da kuma faɗaɗa aikin jamián bada taimako na Majalisar ɗinkin duniya UNAMI a ƙasar Iraqi. Bugu da ƙari ƙudirin ya kuma buƙaci wakilan Majalisar ɗinkin duniya dana UNAMI a Iraqin su bada shawara tare da taimakawa gwamnatin Iraqi ta fannoni da dama da suka haɗa da Siyasa harkokin zaɓe da tsara daftarin kundin tsarin mulki da harkokin shariá da tattalin arziki da kare haƙƙin bil Adama da kuma taimakawa yan gudun hijirar Iraqin komawa zuwa gidajen su. Daftarin na zama ƙarin tagomashi ne ga ƙoƙarin sojin haɗaka da Amurka kewa jagoranci na bada kariya ga jamián Majalisar dinkin duniyar ( UNAMI ) bisa laákari da muhimmancin tsaro wajen samun sukunin gudanar da ayyukan su a madadin alúmar Iraqi.