Da lama sauki ya fara zuwar wa Mr Sharon | Labarai | DW | 11.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Da lama sauki ya fara zuwar wa Mr Sharon

Likitocin dake kula da Faraminista Ariel Sharon sun sanar da shirin fara dawo da Sharon cikin kafatanin hayyacin sa, wanda ke a matsayin na karshe, bayan da suka sumar dashi don gudanar da aiki a cikin kwakwalwar sa.

Wannan shirin dai a cewar ma´aikatan asibitin nada alaka da ci gaba da aka samu ne a aikin da aka yiwa Sharon a cikin kwakwalwar tasa.

A cewar likitocin ,Mr Sharon ya dan juya hannun sa na hagu kana a hannu daya kuma ya amsa wasu maganganu da dan sa yayi masa.

Ya zuwa yanzu dai likitocin sun tabbatar da cewa Mr Sharon ya fita daga cikin matsanancin hali da yake ciki , idan aka kwatanta da halin da yake a yan kwanakin baya, to sai dai kuma tabbatar da ingancin kwakwalwar tasa a cewar su ka iya daukar kwanaki .