Da gaske ne akwai Mota mai amfani da lantarki maimakon Mai | Amsoshin takardunku | DW | 28.04.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Da gaske ne akwai Mota mai amfani da lantarki maimakon Mai

Bayani game da Mota mai amfani da lantarki a maimakon man Fetur ko Gas da aka sani

default

Motar Toyota ƙirar "Hybrid"

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Saudatu Abdul jalal Kazaure a tarayyar Nigeria,Malamar ta ce wai don Allah da gaske akwai mota mai anfani da lantarki a maimakon man fetur ko gas da aka sani?

Amsa:To Malama Saudatu ina fata kina kusa da akwatin Radion ki a daidai wannan lokaci domin sauraron amsar tambayarki. To dai babu shakka da akwai motar da aka ƙera da ke amfani da lantarki to amma fa ba wai ta dogara ga lantarkin ne zalla ba, domin kuwa tana haɗawa da mai kamar sauran motoci. Wannan nau'in mota ita ce turawa suka yiwa lakabi da ƙirar HYBRID, Wanda ke nufin wani abu da aka hada shi ta amfani da fasaha fiye da ɗaya wanda zai tamaka masa wajen yin aiki.

To ita dai wannan mota kamar yadda aka ji a bayanin farko ta dogara ne da nau'in makamashi biyu lantarki da kuma mai sabili da gamayyar fasaha da aka tsara a cikin injinta wanda zai ba ta damar yin hakan. Haka kuma injinta ƙarami ne ba kamar sauran ba. Yadda take haɗa waɗannan makamashi guda biyu dai shi ne, a duk lokacin da aka ta da ita, tana tashi ne da mai to amma da zarar ta fara gudu ta buƙaci ƙarin wuta mai makon mai da zata ƙara sha, sai ta koma kan karfin lantarki da batirinta ke samarwa. A taƙaice dai mota ce da ke da ƙarancin amfani da mai akan sauran motoci.

Kamfanonin ƙera motoci dai sun fuskanci wasu matsaloli da suka tilasta masu tunanin samun mafita wajen cigaba da ƙera motoci. Matsalar farko ita ce ta cigaba da tsada ko kuma hauhawar farashin da mai ke yi da kuma batun gurbata yanayi da hayaƙi yake yi. To sakamakon matsalar farko ta farashin mai ne masana ta fannin kimiya da kuma masu masana'antun ƙera motoci suka shiga binciken hanyoyin samar da mai iri daban-daban da mota za ta iya amfani da su. Ɗaya daga cikin fasahar da suka iya ganowa ita ce ta yin amfani da lantaki da Batir da kuma hayaki ko kuma wutar da mota kan samar a lokacin da aka tashe ta.

Babu shakka gano wannan fasaha ta taka rawar gani domin kuwa ta taimaka masu wajen jifan tsuntsu biyu da dutse guda. Domin kuwa bincike ya nuna cewa baya ga rashin shan mai da wannan nau'in mota ta ke da shi, tana da sauƙin gurbata yanayi akan sauran motoci. Bugu da ƙari kuma wannan nau'in mota an mata tsarin sifa na keta iska yadda za ta iya gudu sosai. wato ƙarama ce mara nauyi tayoyinta ƙarfafa kuma matsakaita.


To kamfanonin motoci irin su Toyota, Honda da Ford na daga cikin waɗanda suke ƙera motar da ke amfani da lantaki da mai a tare. Ƙiyasin da aka fitar na kasuwar motoci a shekara ta 2004 ya nuna cewar daga cikin motoci miliyan 17 da aka sayar a shekar, guda 80,000 ƙirar Hybrid ne. Da kuma shekara ta zagayo a 2005 an gano cewar buƙatar irin wannan mota ya ƙaru inda adadin wanda aka siya ya kai kimanin 200,000. Zuwa shekar bara kuwa, wato shekara ta 2008, adadin da aka sayar ya kai 400,000. kuma har yanzu tagomashinta sai ƙara gaba yake yi.