1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Da alamun shugaban Isra’ila Moshe Katsav ya yi murabus, idan aka ɗuakaka ƙararsa game da zargin fyaɗen da ake yi masa.

October 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bufi

A wata sabuwa kuma, har ila yau dai a Isra’ilan, a halin da ake ciki, shugaban Ƙasar, Moshe Katsav, ya ƙaurace wa shagulgulan buɗe taron majalisar yau, bayan da hukumar ’yan sandan ƙasar ta ba da shawarar a ɗaukaka ƙararsa gaban kotu, saboda zargin fyaɗe da ake yi masa.

Tun jiya ne dai jami’an bincike na wani rukunin ’yan sandan Isra’ilan suka ce sun samo hujjojin da ke tabbatad da zargin da ake yi wa shugaban Moshe Katsav, na fyaɗe. Bayan kammala binciken da suka yi, jami’an sun ce an sami hujjoji da dama da ke nuna aikata laifuffukan fyaɗe ga ma’aikatan hukuma mata, da shugaban ya yi. Ban da haka kuma, ana zarginsa da maguɗi da kuma jiyo maganganun wayan tarho ba bisa ƙa’ida ba. A halin yanzu dai ana jira ne a ga ko, bayan nazarin rahoton ’yan sandan, babban lauyan gwamnati Menachem Masus, zai kai ƙarar shugaban gaban kotu. Shi dai shugaba Katzav da kansa yana watsi da tuhumar da ake yi masa. Amma lauyansa, ya faɗa wa maneman labarai a Birnin Ƙudus cewa, idan aka ɗaukaka ƙarasa gaban kotu, to zai yi murabus.