Da alamu an kusa warware rikicin lardin Darfur dake yammacin Sudan
May 12, 2006Talla
Bisa ga dukkan alamu gwamnatin Sudan zata mika kai ga bukatun kungiyoyin ´yan tawayen nan biyu, wadanda suka ki sanya hannu kan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiyar yankin Darfur a makon jiya. Shugaban babbar kungiyar ´yan tawaye ta Sudanese Liberation Army, Abdel Waheed Mohammed al-Nur ya ce ya samu wata amsa mai karfafa guiwa daga gwamnatin Khartoum a dangane da shawarwarin da ya bayar a ranar laraba, wadda ta nemi gwamnati ta biya diyya mai yawa ga al´uman yankin na Darfur. A cikin makon jiya aka sanya hannu kan yarjejeniyar a birnin Abujan Nijeriya tsakanin gwamnatin Sudan da babbar kungiyar ´yan tawayen Darfur, da nufin kawo karshen yakin da aka shafe shekaru 3 ana yi a wannan yanki.