Da alama, masu neman ´yancin Montenegro daga Sabiya sun yi nasara | Labarai | DW | 22.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Da alama, masu neman ´yancin Montenegro daga Sabiya sun yi nasara

Firaministan Montenegro Milo Djukanovic ya bayyana bangarensa dake goyon bayan ballewa daga tarayyar Sabiya da cewa shi ya yi nasara a kuri´ar raba gardama kan samun ´yancin Montenegro da aka kada jiya lahadi. Wata sanarwar da ya bayar bayan an kammala kidayar kashi 99 cikin 100 na yawan kuri´un da aka kada, FM Djukanovic ya ce ´yan son awaren sun samu kashi 55.5 cikin 100. To sai dai masu adawa da ballewa daga Sabiya sun ce zasu jira har sai hukuma ta ba da sakamakon zaben. A wani lokaci yau din nan za´a ba da sakamakon karshe na kuri´ar raba gardamar.