Da alama bin Laden na nan da ransa | Labarai | DW | 08.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Da alama bin Laden na nan da ransa

Babban kwamandan sojin Amurka a Afghanistan yace da alama shugaban kungiyyar Alqeeda wato Usama Bin laden na nan da ransa bai mutu ba.

Wannan kalamin dai na Janaral Karl yazo ne bayan hasashen da ake na cewa Usama Bin Laden ya rasa ransa a sakamakon girgizar kasar nan da akayi a kasar Pakistan a watan oktoba na wannan shekara.

Janaral Karl ya kara da cewa ya zuwa yanzu babu wani gamsasshen bayani dake nuni da cewa Usama ya mutu. Matukar kuwa yana raye a cewar kwamandan, to babu shakka zasu kamo shi wala, Allah a raye ko kuma a mace.

Bisa dai hasashe da akayi a can baya an dauka Usama Bin Laden na boye ne a cikin tsaunukan kasar Pakistan.