1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Da aiki wajen dakile yaduwar nukiliya

Kamaluddeen SaniApril 2, 2016

Shugabannin duniya da ke halartar taro a Amirka kan dakile yawaitar bazuwar makaman nukiliya a duniya sun ce akwai jan aiki a gaba.

https://p.dw.com/p/1IOXX
Washington Nuklear-Gipfel Plenarsitzung Barack Obama Rede
Hoto: Reuters/K. Lamarque

A daidai lokacin da ake kammala babban taron kwanaki biyu kan takaita makaman nukiliya a birnin Washington na Amirka da shugabannin duniya 20 suka halarta ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shugabannin sun jaddada cewar akwai bukatar tashi tsaye sosai domin dakile sinadaren kera makaman nukilya.

A yayin jawabin karshe ga mahalarta taron Shugaba Barack Obama ya yi amfani da damar wajen yin kira ga kasashen Indiya da Pakistan da su rage sinadaren nukiliyarsu, inda ya ce:

"Kamar yadda na fada a baya aiyukanmu bas u kammala ba, har yanzu muna da gagarumin aiki a gabanmu wajen magance bazuwar sinadaren nukuliya a duniya, a daidai lokacin da sinadaren makamishin nukiliyar ke cigaba da fadada a wasu kasashen duniya."

Mahalarta taron dai sun kuma jaddada cewar dole ne a hada hannu wajen tabbatar da zaman lafiya gami da daukar matakan dakile bazuwar makaman nukiliya da ke barazana ga zaman lafiyar duniya.