1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daƙile ayyukan tarzoma a Sahel

October 25, 2010

Ƙasashen Turai za su taimakawa ƙasashen Sahel wajen yaki da ta'addanci

https://p.dw.com/p/Pnqp
'Yan tarzoma da sunan addiniHoto: AP

Ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai sun yi alƙawarin taimakawa ƙasashen Sahel da kayan aiki domin yaki da ta'addancin na 'yan ƙungiyar Al-Qaida reshen Magreb dake zaman barazana akan al'amuran tsaro a yankin.

Ministocin harkokin waje na ƙasashen ƙungiyar ta EU da suka kammala taronsu a ƙasar Luxemburg sun ummarci jagorar diflomasiya ta ƙungiyar Catherine Ashthon da ta tsara wasu hanyoyi ta fannin dubaru ɓulloma lamarin na ta'addanci na ƙasashen Sahel namn gaba a farkon shekara mai zuwa.

Ko da shike ƙungiyar ta EU ba ta bayar da wani cikkaken bayani ba, amma masu lura da al'amuran yau da gobe na hasashen cewa ɗaukar matakin ba zai rasa nasaba ba da yadda ƙungiyar 'yan tawayen ta Aqmi ta yi sayu a cikin ƙasashen, inda yanzu haka 'yan ta'addar ke yin garkuwa da wasu 'yan ƙasar Faransa guda biyar da ɗaya ɗan Togo da kuma ɗan Madagaska waɗanda Aqmi ta sace tun a tsakiyar watan Satumba da ya gabata.

Mawallafi: Abdourrahmane Hassane

Edita: Mohammad Nasiru Awal