1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar sukari na karuwa a Afirka

Al-Amin Suleiman Mohammad/ MNAApril 7, 2016

Mutane sama da miliyan 400 a fadin duniya ke fama da cutar sukari ta kuma ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane miliyan daya da rabi a shekarar 2012.

https://p.dw.com/p/1IRRq
12.11.2015 DW fit und gesund Diabetes_Teaser

Ranar bakwai ga watan Afrilun kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin bukin Ranar Lafiya ta Duniya da nufin yin duba ga kokarin da hukumomi ke yi ko akasin haka a bangaren bunkasa harkokin lafiya.

Taken bukin na wannan dai shi ne yaki domin kawar da cutar sukari wato Diabetes a turance, wanda kimanin mutane miliyan 400 a fadin duniya ke fama da ita, wanda kuma alkalumma suka tabbatar ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane miliyan daya da rabi a shekara ta 2012.

Masana sun ayyana cewa cutar sukari ko Diabetes ta na barna doron kasa fiye da yadda sauran cututtuka ke yi fiye ma da cutar nan mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS musamman saboda yadda take saurin nakasa sassan jikin bani Adama.

Cuta mai kisa sannu a hankali

Martin-Luther-Universität Halle - Blutuntersuchung
Gwajin jini na daga cikin gwaje-gwajen da ake wa masu cutar sukariHoto: picture-alliance/dpa/W. Grubitzsch

Babbar matsala na wannan cuta shi ne na rashin bayyanar ta da wuri har sai ta kai shekaru 10 da fara illa ga mai dauke da ita kamar yadda Dr Ibrahim Musa Yola na asibitin koyarwa na gwamnatin tarayyar Najeriya da ke garin Gombe ya yi bayani.

"Yawanci illar a hankali take yi. Sugar da baya barin cikin jini shi yake daskarewa a hanyoyin jini. Su kuma kananan hanyoyin jinin sai su fara toshewa, suna kuma lalacewa yadda hakan ke kashe gaba ba a sani ba. Cutar a hankali take akshe mutum."

Masu fama da wannan cuta dai sun nuna cewar suna samun matsaloli musamman na kashe makudan kudade wajen gwaje-gwaje da kuma magunguna kuma babu wani rangwame da gwamnati ke yi wa masu wannan cuta, ko da kuwa na dauke musu kudin gwaji ne.

Abubakar Garba Hamisu Barwan Bogo daya daga cikin masu fama da wannan cuta ne.

"A baya muna gwadawa a kan Naira 300 amma yanzu ya haura zuwa Naira 700. Kuma ana son kusan kullum ka je ka gwada yawan suga a cikin jininka. Saboda kudin ya yi yawa mutane suna samun matsala a wannan bangaren. Magungunan kuma ba sa tabuwa, suna da tsada. Shi yasa cutar tana wahalar da mutane musamman ma talakawa."

Wayar da kan jama'a kan kula da lafiya

Hukumomi dai sun yi imanin cewa fadakar da jama'a yadda za su kiyaye kamuwa da wannan cuta da kuma kiyaye ka'idojin da likitoci suka zayyana wa masu dauke da cutar shi ne mafi muhimmanci wajen yaki da cutar.

Diabetes-Untersuchung in Südafrika
Auna jinin mutane kyauta a Afirka ta Kudu ko suna da cutar sukariHoto: picture alliance/Photoshot

Alhaji Mato Yakubu Dukku shi ne daraktan hukumar wayar da kan al'umma ta kasa da ke Gombe ya yi bayanin irin kokarin da suke na fadakar da al'umma kan wannan cuta da sauran cututtuka.

"Gwamnati tana iya kokarinta donn tabbatar da cewa duk abinda zai kawo wa al'umma illa a yi bayani a kai saboda a fadakar da jama'a. Kiyayewa da kuma bin shawarwarin da likita ya bayar suna da muhimmanci."

Masana dai sun bayyana cewar babu takamaimai hanya ta kamuwa da wannan cuta sai dai sun tabbatar da cewa ana gadon ta kuma sakaci wajen tsara cin abinci da rashin motsa jiki ma na haifar da cutar ko kuma ta'azzara ta. Sun nemi jama'a su gaggauta zuwa wajen likita da zarar sun fara ganin alamu na yawan shan ruwa da yawan cin abinci da kuma yawan yin fitsari da ya zarce yada mutum yake a baya domin tantance ko mutum yana dauke da cutar.