Cutar Sanƙarau na barazana ga ƙasashe 14 a Afrika | Labarai | DW | 20.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar Sanƙarau na barazana ga ƙasashe 14 a Afrika

Ƙungiyyar agaji ta Red Cross ta gargadi ƙasashe 14 a Afrika, dangane da ɓarkewar cutar Sanƙarau. Don kaucewa wannan annoba, ƙungiyyar ta Red Cross ta ɓukaci ƙasashen ɗaukar matakan rigakafi, wanda hausawa kance yafi magani. A yanzu haka dai ƙungiyyar ta Red Cross na shirin ƙaddamar da gagarumin kamfe na yaƙi da wannan cuta a waɗannan ƙasashe. Rahotanni sun ce Ƙungiyyar ta Red Cross na shirin kashe Dolar Amirka dubu 867 kan wannan aiki. Wasu daga cikin ƙasashen da wannan cuta ta Sanƙarau kewa barazana sun haɗar da Nijeriya da Nijar da Ivory Coast da Kenya da Habasha da kuma Sudan.