Cutar Murra tsintsaye a nahiyar turai | Labarai | DW | 23.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar Murra tsintsaye a nahiyar turai

Barazanar yaduwar cutar murra tsintsaye na kara tada hankulla jama´a a nahiyar turai.

Bayan tsintsayen daji bincike ya gano cewar na gidan ma bas u tsira ba, inda karo na farko a ka gano wasu agwagi 2 da alamomin kamuwa da wannan cuta.

A nan Jamus agwagi 110 su ka mutu a sanadiyar cutar murra tsintsaye., mafi yawan su a tsibirin Rügen da ke arewa maso gabacin ƙasar.

A fadar mulkin Gwammnati da ke Berlin, ministan taraya mai kulla da harakokin noma Horst Seehofer, da takwarorin sa na jihohi, su yi zaman taro, domin tunani a kan mattakan biya, idan cutar ta fara bulla daga tsintsaye zuwa dan Adam.