1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar murar tsuntsaye ta kaseh wasu mata biyu a Indonesia

January 13, 2007
https://p.dw.com/p/BuUh
Wasu mata biyu ´yan kasar Indonesia sun rasu sakamakon kamuwa da cutar murar tsuntsaye, wadda ta sake kunno kai kwanan nan a cikin kasar. Wani jami´in ma´aikatar kiwon lafiya ya ce daya daga cikin matan ta rasu a jiya juma´a yayin da dayar kuma ta cika da sanyin safiyar yau asabar. Dukkan su biyu ana yi musu jiya ne a wani asibiti dake Jakarta babban birnin kasar.