1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar murar tsuntsaye a Koriya ta kudu

December 13, 2006
https://p.dw.com/p/BuY5

Hukumomin kasar Koriya ta kudu sun kammala kashe dubban daruruwan kaji da dangoginsu ayau,bayan an sake samun bullar murar tsuntsaye a karo na uku,cikin tsukukin wata guda.Kimanin kaji da dangoginsu dubu 365 ne aka kashe su a gidan gona dake Gimje,mai tazar km 262 kudancin birnin Souel ,sakamakon tabbatar da bullar cutar a ranar litinin.Wanda kuma ya kawo ga adadin kaji million 1.3 kenan aka kashe da sanar da bullar murar´a watan daya gabata.Kawo yanzu dai ana cigaba da binciken sinadarin cutar mai nauin H5 N1.