Cutar massasara kaji a nahiyar Afrika | Labarai | DW | 14.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar massasara kaji a nahiyar Afrika

Rahotani daga Tarayya Nigeria, na nuna kara yaduwar cutar mura tsintsaye, da ta barke a kasar, satin da ya gabata.

Jami´an kiwon lahia na Ikko, birni mafi girma a nahiyar Afrika, sun bayyana daura damara yakar wannan cuta, duk da cewar, ya zuwa yanzu, babu mutum ko daya, ko kuma wani tsuntsu da ya kamu da cutar.

Jami´an kiwon lahia sun kaddamar da Kampain, domin fadakar da jama´a bisa mattakan riga kafi.

Wasu rahotanin kuma, na nunar da cewa, da dama daga makiyayen kaji a arewancin Nigeria, na shigar da kajin su zuwa makwabciya jamhuriya Benin inda su ka fi parashe.

Tun bayan hiddo sanarwar massasara kaji, kasuwar su ta fadi, a tarayya Nigeria.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Benin, ya karayata wannan batu, ya kuma shaida cewa humumomin kiwon lahia na jihohin da ke iyaka da Nigeria, sun dauki matakan karfafa bincike, domin hana shigowa da kaji.

A cemma kasar Senegal shugaba Abdulahi Wade yayi jawabi na mussaman, zuwa ga al´umma kasa, a game da wannan cuta.

Shugaban ya bukaci jama´ata yi anfani da mattakan riga kafi da gwamnati ta tanada, don gudun kamuwa da cutar massara tsintsaye da ke matsayin babar illa ga tattalin arzikin kasa.