1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Lassa ta kashe mutane 100 a Najeriya

Yusuf Bala Nayaya
April 16, 2018

Mutane 101 ne suka halaka bayan barkewar mummunar cutar zazzabin Lassa a Najeriya kamar yadda kungiyar likitoci nagari na kowa (MSF) ta bayyana a ranar Litinin.

https://p.dw.com/p/2w80T
Nigeria | Krankenhaus in Abuja
Babban asibitin Abuja a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Sama da mutane 400 ne suka harbu da kwayoyin cutar mai hadarin gaske tun daga watan Janairu inda ta kai ga bazuwa a jihohi 18 na kasar da ke a yankin yammacin Afirka, kamar yadda kungiyar ta MSF ta bayyana. Jihohin da abin yafi munana sun hadar da jihar Ebonyi Kudu maso Gabashin Najeriya da jihar Bauchi Arewa maso Gabashi da Ondo a Kudu maso Yammaci a cewar ta likitocin kungiyar MSF. Ta kara da cewa baya ga marasa lafiyar da ke mutuwa har ma da likitocin da suke dubasu.

Zazzabin na Lassa dai na samuwa ne ta hanyar mu'amala da abinci ko wasu abubuwan da beran da ke baza cutar ya yi bayan gari a jikinsu, haka kuma mu'amala da jini ko bayan gida da sauran abubuwan da suka fita daga mutumin da ya kamu da cutar.