Cutar kwalara a kasar Benin | Labarai | DW | 19.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar kwalara a kasar Benin

Opishin ministan kiwan lahia na Benin, ya bayyana yaduwar cutar Kwalara a wannan kasa.

Annobar ta bullo tun watan july da ya wuce.

A halin da ake ciki, binciken da malluan kiwan lahia su ka gudanar, ya gano mutane 460 dasu ka kamu da cutar.9 daga cikin su, sun riga mu gidan gaskiya.

A karshen watan satumber da ya gabata, hukumar majalisar dinkin dunia, mai kulla da lahiyar al´umma, ta bayana damuwa a game da yaduwar annobar kwalara a kasashe 8 na yammacin Afrika, inda mutane dubu 46, su ka kamu da ita, wanda daga cikin su, 800 su ka kwanta dama.